Bidiyon jerin gwano motocin da suka yi wa shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu rakiya a lokacin da ya sauka a jihar Legas ya tayar da kura, inda jama’a ke ta cece-kuce a shafukan sada zumunta.
Shaidu sun ce sabon shugaban kasar ya samu rakiyar motoci sama da dari bayan dawowa daga Birtaniya domin gudanar da bikin Babbar Sallah a Legas.
Kazalika an ga gwamman motocin soji na masa rakiya a hanyoyin da aka rufe aka hana kowa wucewa, abin da ya haifar da gagarumin cunkoso.