Shugaba Bola Tinubu ya isa Kigali a Rwanda a ranar Laraba, gabanin fara taron manyan jami’an gudanar da kamfanonin Afirka karo na 13 (Africa CEO Forum), wanda za a fara a ranar Alhamis.
Shugaban ya samu tarba daga Ministan Harkokin Waje, Ambasada Bianca Ojukwu, da Ministan Tsaron Rwanda, Juvenal Marizamunda, a filin jirgin sama na kasa da kasa dake Kigali.
Sauran wadanda suka zo tarbar shugaban sun hada da Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dr. Jumoke Oduwole, Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ambasada Mohammed, Jakadan Najeriya a Rwanda, Ambasada Ibrahim Zanna, da Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Kafofin Yada Labarai da Sadarwar Jama’a, Chief Sunday Dare.
An fara taron a shekarar 2012 da Jeune Afrique Media da Hukumar Kudi ta Duniya (IFC) ke shirya shi, kuma ya zama taro mafi girma na shekara na shugabannin kamfanoni masu zaman kansu na Afirka, masu zuba jari, da masu tsara manufofi. Taron na mai da hankali ne kan hanzarta sauyin tattalin arziki ta hanyar raba girma, hadin kan yanki, da kara zuba jari tsakanin kasashe.
Shugaba Tinubu zai yi amfani da damar taron wajen sake tabbatar da kudurin Najeriya na cigaba da hada kan Afirka, karfafa hadin gwiwar tattalin arzikin yanki, da hadin gwiwa don samar da ci gaba mai dorewa da masu zaman kansu ke jagoranta a fadin nahiyar.











































