‘Yan sanda sun kama wata mata da ake zargi da kona kishiya da ‘ya’yanta a Kano

Police olopa new 750x430

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta kama wata mata mai shekaru 32, Maryam Usman, da ake zargi da kona dakin kishiyarta a unguwar Mangwarori, yankin Mariri da ke Kano, inda mutum hudu suka jikkata da mummunan kuna.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya sanya wa hannu a ranar Laraba, ya ce lamarin ya faru ne da cikin daren ranar 12 ga Mayu na shekarar 2026, lokacin da rundunar ta samu kiran neman taimako da karfe 12:40 na dare.

Ya bayyana cewa wanda ake zargin da kona dakin da kishiyarta Firdausi Saminu mai shekaru 40 ke zaune.

A cewar sanarwar, mutum hudu ciki har da kishiyar da ‘ya’yanta biyu masu shekaru uku da biyar, da mijinsu Saminu Miko, sun samu munanan kunar daban-daban sakamakon wutar.

“An gaggauta kai su asibiti don samun kulawar gaggawa,” in ji mai magana da yawun ‘yan sandan, inda ya ce yanzu haka ana jinyar wadanda lamarin ya rutsa da su a Asibitin Kwararru na Sir Sunusi da ke Kano.

Rundunarr ta kara da cewa tawagarta jami’anta na sintiri sun isa wurin da gaggawa, lamarin da ya kai ga kama wanda ake zargin a wurin.

‘Yan sanda sun kuma bukaci jama’a da su warware sabanin gida cikin lumana ta hanyar tattaunawa da hanyoyin al’umma da suka dace, suna mai gargadin cewa tashin hankali da kona gida laifuka ne da doka ke hukunci a kai.

Rundunar ta kara karfafa mazauna yankin da su rika kai rahoto game da alamun rikicin gida ga hukumomin tsaro ko shugabannin al’umma domin hana yaduwarsa, da kuma kaucewa daukar doka a hannunsu.

Ta sake tabbatar da aniyarta ta kare rayuka da dukiya, tana mai rokon jama’a da su rika kai rahoto kan duk wani abu da ake zargi ko barazana ta layukan gaggawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here