Rikicin APC Kano: G7 sun dage sai an yi gaskiya, adalci, samar da daidaito wajen rabon mukamai

5B3D6829 3123 44A2 ACF3 A78E5B3899F7
5B3D6829 3123 44A2 ACF3 A78E5B3899F7

Bangaren jam’iyyar APC na Sanata Ibrahim Shekarau, sun jaddada kudirinsu na ganin an yi sulhu da bangaren gwamna Ganduje, inda suna jaddada cewa za su  amince da sulhu matukar aka yi Gaskiya da adalci, sannan aka samar da daidaito.

Hedikwatar jam’iyyar APC karkashin jagorancin shugaban riko, Mai Mala Buni a ranar Asabar din da ta gabata sun sake yin wata ganawa da bangarorin biyu, inda jam’iyyar ta bayyana cewa za ta samar da wani jadawali wanda zai taimaka wajen rabawa bangarorin biyu mukaman jam’iyyar, wanda ake sa ran a wannan litinin din kwamitin zai zo Kano domin fara wannan aikin.

Har ila yau, a ranar Lahadin da ta gabata ne shugaban G7 kamar yadda ake kiran  bangaren, Sanata Ibrahim Shekarau ya fitar da wani faifan faifan murya yana mai jaddada muhimmancin yin sulhu inda ya ambaci ayoyi kusan uku na Alkur’ani mai girma.

Sai dai a wata sanarwar hadin gwiwa da manyan jagororib 7 suka sanyawa hannu a ranar Lahadi mai taken ”Joint Stakeholders Forum of All Progressive Congress) jihar Kano, ta bayyana cewa ”Muna so mu bayyana cewa ba shakka, har zuwa wannan lokaci na fitar da wannan wannan sanarwa ba a yanke hukunci na karshe dangane da sulhun da ke gudana ba.”

Solacebase ta rahoto cewa mambobin da suka sanya hannu a takardar sun hada da Sanata lbrahim Shakarau, (Kano ta tsakiya), Sanata Barau l. Jibrin,(Kano North), Tijjani Abdulkadir Jobe,(Dawakin Tofa/Tofa/Rimigado), Nasiru Abduwa Gabasawa,(Gezawa/Gabasawa) Barista. Haruna l. Dederi, (Karaye/Rogo), Sha’aban Sharada, (Kano Municipal) da Alh. Shehu Dalhatu (Shugaban kungiyar Buhari Support Group.)

Sanarwar ta kara da cewa, “Kowa ya san irin kokarin da Shugabancin jam’iyyarmu ta kasa ke yi  da nufin lalubo hanyoyin da za a bi wajen warware rigingimun da suka dabaibaye babbar jam’iyyar mu reshen Jihar Kano, muna so mu yaba da wannan gagarumin shiri na jam’iyyar a matakin kasa ke yi.

Sanarwar ta ce, ”Wannan duk kuwa da cewa mun ci gajiyar hukunce-hukunce guda biyu a cikin cikin kara mai lamba Nos. 2021 dangane da shugabancin jam’iyyar a jihar mu.”

“Muna kira ga kowane dan jam’iyyar a jihar Kano da ya kwantar da hankalinsa tare da biyayya ga jam’iyyar har sai an kawo karshen zaman sulhu,” in ji sanarwar.

Kungiyar a cikin sanarwar ta kara da cewa, ”Muna kara tabbatar da goyon bayanmu da jajircewarmu ga ci gaban akidar babbar jam’iyyar mu Jam’iyyar APC a jihar Kano da ma Najeriya baki daya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here