Kotu ta hana wata karamar hukuma a Kano karbe gonakin manoma 370

WhatsApp Image 2022 04 05 at 2.01.26 PM
WhatsApp Image 2022 04 05 at 2.01.26 PM

 

Wata babbar kotun Kano ta hana karamar hukumar Madobi da shugabanta Muhammad Lawan Yahaya da gwamnatin jihar da wasu mutane hudu karbar filayen noma a unguwar Kafin-Agur da ke yankin Madobi a jihar.

Alkalin kotun, Mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya bayar da umarnin a ranar Talata a karar da Yunusa Abdulmuminu da wasu 369 suka shigar.

Wadanda ake kara a karar su ne Muhammad Lawan Yahaya, shugaban karamar hukumar Madobi, karamar hukumar Madobi, hukumar tsare-tsare da raya birane ta jihar Kano (KNUPDA), ofishin kula da filaye Kano, babban lauyan gwamnatin jihar Kano, gwamnatin jihar Kano. da kuma kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano.

Solacebase ta ruwaito cewa masu shigar da kara na zargin wadanda ake kara da karfin kwace filayen noman su, a karamar hukumar.

An bayar da wannan umarnin ne biyo bayan wani kudiri na sakin layi na 27 da Barista Abba Hikima ya shigar tare da rantsuwar Yunusa Abdulmuminu.

Mai shari’a Ma’aji ya hana wadanda ake kara ko masu kara ko kuma wakilansu bayyana kansu a matsayin masu gonakin

dako kuma kutsa kai cikin gonakin har zuwa lokacin da za a saurari karar da kuma yanke hukunci.

Alkalin kotun ya kuma bayar da umarnin dakatar da wanda ake kara na 7 wato kwamishinan ‘yan sandan Kano, daga kamawa ko musgunawa ko tura mutanensa domin kwacewa daga masu ikirarin mallakar gonakin.

Daga nan an dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga Afrilu, 2022 don sauraron karar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here