Akpabio ya fallasa gwamnoni da karbar Naira Biliyan 30

Godswill Akpabio, fallasa, karbar, gwamnoni, Naira, Miliyan
Shugaban majalisar dattawan Najeriya Godswill Akpabio, ya fallasa gwamnonin jihohin kasar, inda ya ce kowannensu ya karbi Naira biliyan 30 daga asusun...

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Godswill Akpabio, ya fallasa gwamnonin jihohin kasar, inda ya ce kowannensu ya karbi Naira biliyan 30 daga asusun tarayya domin inganta hauhawar farashin kayayyaki da tsadar abinci a jihohinsu.

Yayin da gwamnatin tarayya ta ce an saki Naira biliyan 2 ga gwamnoni daga cikin rancen Naira biliyan 5 da ta baiwa kowace jiha a matsayin tallafi don rage tasirin cire tallafin man fetur.

Karanta wannan: Somaliya ta amince da yarjejeniyar tsaro da Turkiyya

Akpabio ya ce bayanan da ya samu sun nuna cewa an aike da karin Naira biliyan 30 zuwa gare su ta hanyar ma’aikatar harajin cikin gida ta tarayya FIRS.

Sai dai ya shawarci gwamnonin da su yi amfani da kudaden cikin adalci wajen rage tsadar kayan abinci da sauran kalubalen da kasar ke fuskanta.

“Mun yi imanin cewa ya kamata kowace gwamnatin jiha ta yi amfani da kudaden da aka samu wajen ganin an samu abinci a kasar nan. Don haka gwamnatocin jihohi suna da yawa” inji shi.

Karanta wannan: Majalisar dattawa za ta binciki Emefiele da tsohuwar gwamnatin Buhari

Ya kara da cewa, “Sun fi kusanci da jama’a kuma ba na son in ambaci kananan hukumomi domin yawancin kananan hukumomin gwamnonin jihohi ne ke rike da su.

“Aiki na shi ne idan har gwamnatin jiha ta yi abin da ake bukata, to karamar hukumar za ta sa hannu a raba don ganin wadannan abubuwa sun isa ga jama’a. Amma kada mu manta da cewa ’yan Najeriya ba za su yi sha’awar labarai ba.

“Yan Najeriya na son ganin mataki haka ’yan Najeriya suna son su ci su koshi, mu kuma za mu ba su abinci” in ji Akpabio.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here