JAMB ta fara rajistar neman gurbin NCE da fannonin aikin gona da ba na fasaha ba

JAMB 2

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandare ta Ƙasa (JAMB) ta fara yin rajistar ga dalibai masu neman gurbin shiga manyan makarantun horar da malamai domin samun shaidar zama malami (NCE), da kuma fannonin aikin gona da ba na fasaha ba a kwalejojin kimiya da fasaha a fadin kasar nan.

Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na hukumar, Dr. Fabian Benjamin ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a birnin Tarayya Abuja.

Hukumar ta bukaci dalibai masu sha’awa wadanda ke da bukatun sakamakon jarabawar matakin O’Level da su je su yi rajista a kowace Cibiyar (IPRC) da ke cikin kwalejojin ilimi ko kuma kowace Cibiya ta JAMB (PRC) da ke fadin kasar.

Benjamin ya bayyana cewa, bisa ga manufar Gwamnatin Tarayya, daliban da ke neman gurbin shiga NCE da na Aikin Noma da ba na fasahar zamani ba, ba sa bukatar yin jarrabawar UTME.

Ya bayyana cewa Hukumar ta samar da ingantaccen tsarin shigar da dalibai domin tabbatar da cewa kawai wadanda suka cancanta ne ake shigarwa cikin shirye-shiryen, tare da kiyayewa da inganta ingancinsu da matakin su.

A karkashin sabon tsarin, daliban da suka cancanta suna bukatar su gabatar da takardun O’Level a kowanne IPRC ko JAMB PRC da aka tantance ne kadai domin kammala rajistarsu, ba tare da rubuta jarrabawar UTME ta shekara-shekara ba.

JAMB ta bukaci daliban da suka cancanta da su yi amfani da wannan dama ta hanyar ziyartar wuraren rajista da aka tantance a Kwalejojin Ilimi ko ofisoshin JAMB a fadin kasar domin kammala tsarin rajista.

Hukumar ta kuma sanar da cewa daliban da suka shiga jarrabawar UTME ta 2026 amma yanzu sun yanke shawarar bin shirye-shiryen NCE ko na Aikin Gona za su iya canza aikinsu a kowanne IPRC ko JAMB PRC ba tare da kara biyan kudi ba.

JAMB ta ce manufar ita ce fadada damar samun gurbin karatun NCE da na Aikin Gona, yayin da ake kiyayewa da kuma tabbatar da ingancin wadannan muhimman hanyoyin ilimi.

Hukumar ta sake jaddada kudirinta na tabbatar da tsarin shigar da dalibai mai gaskiya da inganci wanda zai tallafa wa kokarin Gwamnatin Tarayya na karfafa ilimin malamai da samar da kwararru a fannin noma a Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here