Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire JAMB ta ce za ta fara sayar da fom na shiga jami’a kai tsaye ga masu neman shiga manyan makarantu daga ranar Laraba 12 ga Maris, 2025.
Hukumar, a wata sanarwa da kakakin ta Fabian Benjamin ya fitar a ranar Litinin, ta ce wannan rajistar na da matukar muhimmanci ga mutanen da suka mallaki takardar shaidar digiri, ko difloma da sauran su kuma suna son ci gaba da karatunsu a jami’o’in da suka fi so.
”Fara sayar da DE ya biyo bayan nasarar kammala jarrabawar UTME a ranar Asabar, 8 ga Maris, 2025″.
Karin karatu: Ba za mu sake tsawaita lokacin yin rajistar UTME bayan cikar wa’adi – JAMB
“JAMB ta jaddada mahimmancin bin dukkan sharuddan shiga jami’o’i, inda ta yi gargadin cewa za a yi hukunci mai tsanani kan duk wanda aka kama da takarda da ke dauke da bayanan karya.
Za a iya yin rajista ne kawai a Cibiyar Rajista ta JAMB.