Wike, Fubara, Gwamnoni da sauran shugabanni sun yi buda baki tare da Tinubu

tinubu fubara and wike

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi buda baki tare da gwamnan jihar Ribas, Sim Fubara da kuma ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, da sauran gwamnoni, ministoci da shugabannin ma’aikatu, sassa da hukumomi a fadar shugaban kasa ta Villa da ke Abuja.

Buda baki da gwamnoni da Ministoci da shugabannin hukumomi da kuma jami’an tsaro na daga cikin wata al’ada ta shekara-shekara da shugaban kasa ke shirya wa

liyafar cin abincin da aka gudanar a ranar litinin ita ce buda baki na farko da shugaban kasa ya shirya a wannan watan na Ramadan.

Haka kuma a wajen liyafar buda baki akwai mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila da mambobin majalisar ministoci.

Karanta: Hukumar NAHCON ta amince da yin rijistar aikin Hajji a lokacin azumin Ramadan

Daga cikin gwamnonin jihohin da suka halarci taron akwai Dr. Alex Otti na jihar Abia, Fasto Umo Eno na Akwa Ibom, Bala Mohammed na Bauchi, Hyacinth Alia na Benue, Babagana Zulum na Borno, Sheriff Oborevwori na Delta, Monday Okpebholo na Edo, Muhammad Yahaya na Gombe, Umar Namadi na Jigawa da Uba Sani na Kaduna.

Sauran sun hada da Abba Kabir Yusuf na Kano, Nasir Idris na Kebbi, AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara, Abdullahi Sule na Nasarawa, Mohammed Bago na Niger, Dapo Abiodun na Ogun, Lucky Aiyedatiwa na Ondo, Duoye Diri na Bayelsa da Francis Nwifuru na jihar Ebonyi.

Sai kuma shugabannin manyan hukumomin gwamnati irin su shugaban hukumar kula da aikin hajji ta ƙasa Farfesa Abdullahi Mukhtar Muhammad, da mukaddashin Konturola Janar na hukumar Gyaran hali ta ƙasa Sylvester Ndidi Nwakuche, da shugaban hukumar kashe Gobara ta tarayya Jaji Abdulganiyu, da shugaban hukumar Kwastam Bashir Adeniyi.

Shugaban rukunin kamfanin man fetur na kasa NNPCL, Mele Kyari da babban jami’in hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa Farouk Ahmed.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here