images 42

Tsohon Ministan Sadarwa, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya shiga jam’iyyar PDP a hukumance, sannan ya samu tikitin takarar gwamnan jam’iyyar a zaben 2027 a Jihar Gombe.

Pantami ya samu tikitin PDP ta hanyar amincewa da muryar daya a lokacin zaben fidda gwanin jam’iyyar da aka gudanar ranar Talata a Gombe.

Shugaban Kwamitin Zaben PDP, Gregory Yenlong ne ya ayyana Pantami a matsayin dan takara daya tilo, sannan ya sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Da yake jawabi jim kadan bayan tabbatar da shi, Pantami ya ce shawararsa ta tsayawa takar kujerar gwamna ta samo asali ne daga kudurinsa na yi wa mutanen Jihar Gombe hidima.

Ya yi alkawarin samar da shugabanci mai adalci, gaskiya, da tafiya da kowa idan aka zabe shi a matsayin gwamna a 2027.

Pantami zai fafata da Jamilu Gwamna, dan takarar jam’iyyar APC, a zaben gwamna mai zuwa.

Kafin shiga PDP, Pantami ya kalubalanci tsarin da ya fitar da Gwamna a matsayin dan takarar APC na maslaha. Da farko ya nuna aniyarsa ta shiga zaben fidda gwanin APC amma daga baya ya janye kwana guda kafin a gudanar da zaben, inda ya yi zargin rashin gaskiya a tsarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here