Sakataren Jam’iyyar APC na kasa, Ajibola Basiru, ya yi maraba da ayyana dokar ta-baci da shugaba Bola Tinubu ya yi a jihar Rivers.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa Tinubu, a wani jawabi da ya yi a fadin a ranar Talata, ya ayyana dokar ta-baci, saboda tashe-tashen hankula na rikicin siyasa da kuma rahotannin tsaro da ake fuskanta a jihar Rivers.
Tinubu ya bayyana cewa, bayanan da jami’an tsaro suka yi a baya-bayan nan sun nuna yadda tsageru ke lalata bututun mai, ba tare da wani kokarin da gwamnan ya yi na shawo kan lamarin ba.
Da yake mayar da martani kan wannan lamari, magatakardan jam’iyyar APC ya bayyana fatan cewa wannan mataki zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar mai fama da matsalar man fetur.
Basiru ya koka da yadda bangaren zartaswa da na majalisa a Rives suka gaza wajen gudanar da aikinsu bida kundin tsarin mulkin kasa da ya ba su na tabbatar da walwala da tsaron jama’a.
Karin karatu: Babu wani iko a tsarin mulki da ya baka damar tsige Fubara – NBA ta gaya wa Tinubu
Ya shawarci gwamnan Osun da ya lura ya bar kananan hukumomin da kotu ta mayar su aiki, ko kuma su fuskanci irin wannan sanarwar ta gaggawa a Osun.
Shugaban ya umarci hukumomin tsaro da su kiyaye rayuka, dukiya, da muhimman ababen more rayuwa da suka hada da bututun mai a fadin Rivers.
Tuni dai shugaban kasa ya zabi mataimakin gwamnan Admiral Ibok-Ete Ibas (Rtd) a matsayin mai kula da al’amuran jihar Rivers.(NAN)