Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana bakin cikin sa matuka kan rasuwar fitaccen malamin sadarwa, Musa Adamu Labaran, wanda ya rasu a ranar Latinin bayan gajeriyar jinya.
Dr. Labaran, malami ne a Sashen Sadarwa na Jami’ar Bayero Kano, gwamnan ya bayyana shi a matsayin malami mai mutunci wanda gudummawar sa ga karatun sadarwa da ilimin kafafen yada labarai zata bar gibi babba a cikin al’umma.
A cikin sakon ta’aziyyar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Yusuf ya ce marigayin malamin ya sadaukar da rayuwarsa ga koyarwa, bincike, da jagorantar dalibai da kwararru a fadin kasar.
Gwamnan ya bayyans cewa jajircewar Dr. Labaran ga ci gaban ilimi, tattaunawar jama’a, da yada ilimi ya sa ya samu yabo a tsakanin masu ilimi da na kafafen yada labarai.
A cewar sanarwar, gwamnan ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ba ga al’umma makaranta kadai ba, har ma ga harkokin yada labarai da al’umma baki daya.
Ya kara da cewa marigayin ya gadar da nagarta, gaskiya, da hidima ba tare da son kai ba, inda ya jaddada cewa rashinsa zai bar gibi a fannin ilimi da harkokin sadarwa.
Gwamna Yusuf ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya gafarta wa marigayin kurakuransa ya sa shi a Aljannatul Firdaus.
Haka kuma ya mika ta’aziyya ga iyalansa, abokan aikinsa, dalibai, abokan arziki, da sauran al’ummar ilimi bisa wannan rashi.












































