Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta yi Alla-wadai da kisan wasu matafiya da gungun mutane suka yi a jihar Edo.
Wata sanarwa da ta fito daga wajen shugaban ƙungiyar gwamnonin, Muhammad Inuwa Yahaya, ta buƙaci a gudanar da cikakken bincike domin kama waɗanda suka aikata “wannan ta’asar” don hukunta su.
Ƙungiyar ta kwatanta harin a matsayin ƙeta hakkin ɗan’adam, inda ta ce ba za ta lamaunci ɗaukar doka a hannu ba.
Ta kuma jajantawa iyalan waɗanda suka rasa ƴan uwansu a lamarin.
“Mun damu matuka kan kisan bayin Allah da ba su aikata komai ba, da kuma irin yadda aka kashe su,” in ji Inuwa Yahaya wanda kuma ya kasance gwamnan Gombe.
Labari mai alaƙa: Gwamnan Edo ya bada umarnin gudanar da bincike kan kashe matafiya yan Arewa
Ya ce abin da aka aikata ya saɓa wa doka, don haka ya zama dole hukumomi su gudanar da cikakken bincike kan yadda aka kashe mutanen ta hanyar cinna musu wuta.
Gwamna Inuwa Yahaya ya nanata cewa kowane ɗan Najeriya yana da ƴancin yin tafiya zuwa ko’ina, ba tare da nuna bambancin addini ba.
Ya buƙaci gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki matakin da ya dace don hana afkuwar irin haka a nan gaba, inda ya yi kira da a kwantar da hankali.
BBC