Tinubu ya nemi a gaggauta kama waɗanda suka kashe matafiya a Edo

f2950866 c810 40cb bfeb fccdabc130b5.jpg

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi tir da kashe matafiya da aka yi a jihar Edo, inda ya buƙaci a gaggauta nema tare da kama waɗanda suka aikata laifin.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Bayo Onanuga ya fitar yau Alhamis, Tinubu ya bai wa ƴan sanda da sauran jami’an tsaro umarnin gudanar da cikakken bincike da nufin hukunta masu laifi.

“Na kaɗu matuka da jin wannan mummunar labari na kisan wasu matafiya,” in ji Tinubu.

Ya jajantawa iyalan waɗanda aka kashe musu ƴan uwa a lamarin, inda ya tabbatar da cewa ba za a bari ɓata-gari su riƙa zubar da jinin bayin Allah ba a Najeriya.

Karin karatu: Gwamnonin Arewa sun yi Allah wadai da kisan matafiya a Edo

Shugaban ya ce ɗaukar doka a hannu ba shi da muhalli a Najeriya – kuma dukkan ƴan Najeriya na da ƴancin yin tafiya zuwa kowane sassa a faɗin ƙasar.

Ya kuma yaba wa gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo da shugabannin al’umma a jihar bisa ɗaukar matakin domin hana yaɗuwar lamarin.

BBC

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here