Yan sanda sun kama mutane 14 a Edo bisa zargin kashe matafiya 16 ‘yan arewa

Police badge

Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta kama wasu mutane 14 da ake zargi da laifin kisan gillar da aka yi wa matafiya 16 ‘yan arewa da kuma kona motar su a Udune Efandion a ranar Alhamis a kan titin Uromi/Obajana.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Moses Yamu, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Benin, har ma ya yi Allah-wadai da kashe-kashen da aka yi, ya kuma ba da tabbacin za a yi adalci.

Yamu ya bayyana cewa rundunar ta dukufa ne domin tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa.

Ya tabbatar da cewa wata tawagar ‘yan banga ne suka tare wata mota dauke da matafiya 25 daga Elele, jihar Ribas a garin Uromi.

Karanta: Tinubu ya nemi a gaggauta kama waɗanda suka kashe matafiya a Edo

A yayin tsayawar, kakakin ‘yan sandan ya ce an samu wasu matafiya dauke da bindigogi hakan ya haifar da tuhuma a tsakanin ’yan banga.

An ceto goma daga cikin matafiya, biyu daga cikinsu sun samu raunuka an garzaya da su asibiti kuma a halin yanzu suna karbar magani.

A halin da ake ciki kuma, an tura wani sashi na jami’an ‘yan sandan tafi da gidanka zuwa yankin don hana sake karya doka da oda.

A cewar Yamu, kwamishiniyar ‘yan sanda a Edo, Betty Otimenyin, ta bukaci a zauna lafiya a tsakanin kungiyoyi, tare da yim kira ga mazauna garin da su kwantar da hankalinsu tare da ba ‘yan sanda hadin kai, tare da yi gargadi game da duk wani nau’i na harin ramuwar gayya ko tarukan da ba bisa ka’ida ba wanda zai iya haifar da tashin hankali. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here