AFCON: Najeriya ta doke Uganda da ci 3-1 

Super Eagles 1 750x430

Tawagar kungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles ta doke tawagar Cranes ta ƙasar Uganda da ci uku da ɗaya a wasan rukuni na ƙarshe a gasar Kofin ƙasashen Afrika ta shekarar 2025.

Raphael Onyedika ya zura ƙwallaye biyu, yayin da Paul Onuachu ya ƙara ɗaya, abin da ya bai wa Najeriya nasara a kan Uganda da ta rage da ‘yan wasa goma a filin wasa na Stade Foot des Fes da ke ƙasar Morocco a ranar Talata.

Najeriya ta riga ta tabbatar da tsallakewa zuwa zagaye na biyu na gasar, lamarin da ya sa kocin tawagar, Eric Chelle, ya sauya ‘yan wasa takwas daga cikin waɗanda suka fara wasan da ya gabata.

Victor Osimhen, Calvin Bassey da Bruno Onyemaechi kaɗai ne suka ci gaba da kasancewa a jerin ‘yan wasan farko, yayin da Ryan Alebiosu ya fara buga wasansa na farko a Super Eagles a matsayi na baya na dama.

Raphael Onyedika da Fisayo Dele-Basiru sun taka leda a tsakiyar fili, yayin da Samuel Chukwueze da Moses Simon suka yi wasa a gefuna, suna tallafa wa Victor Osimhen da Paul Onuachu a gaba.

Duk da sauye-sauyen ‘yan wasa da aka yi, Najeriya ta rinjayi Uganda, inda ta ci ƙwallo cikin mintuna talatin na farko. Paul Onuachu ya rama kuskuren da ya yi a baya, bayan ya ɓata babbar dama daga kwallon da Victor Osimhen ya ba shi.

Dan wasan kulob din Trabzonspor ya sake samun dama bayan Fisayo Dele-Basiru ya kutsa cikin akwatin bugun fanareti ya mika masa ƙwallo, inda Onuachu ya tura ta wuce mai tsaron ragar Uganda, Denis Onyango.

Bayan hutun rabin lokaci, Uganda ta shiga damuwa, bayan Denis Onyango ya ji rauni a idon sawu, lamarin da ya sa aka maye gurbinsa da Salim Jamal.

Sai dai bayan ‘yan mintuna kaɗan da shigowarsa, Jamal ya kama ƙwallo a wajen akwatin bugun fanareti, abin da ya jawo aka nuna masa jan kati.

Da Uganda ta rage da ‘yan wasa goma, tawagar ta ƙara raunana, Raphael Onyedika ya amfana da wannan yanayi, inda ya zura ƙwallaye biyu cikin kwarewa, tare da taimakon Samuel Chukwueze da ya ba shi damar cin duka ƙwallayen.

Super Eagles ta kammala wasannin rukuni na C da maki tara cif daga wasanni uku. Tunisia ta zo ta biyu a rukunin, yayin da Tanzania ta kuma tsallaka zuwa zagaye na gaba a matsayin ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suka zo na uku mafi kyau.

Najeriya za ta kara da ƙungiyar da ta zo ta uku a rukunin F a wasan zagaye na biyu da za a buga ranar 5 ga watan Janairu, yayin da Ivory Coast, Cameroon da Mozambique ke cikin ƙungiyoyin da ake sa ran ɗaya daga cikinsu za ta fafata da Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here