Zargin Dala Miliyan 9.7 na tallafa wa ta’addanci: EFCC ta shigar da sabuwar ƙara kan kwamishinan kuɗi na Bauchi da wasu mutane

Dr Yakubu Adamu e1765640415332 474x430

Hukumar yaki da yi wa tattalin arziki zagon ƙasa EFCC ta shigar da sabuwar ƙara a ranar Talata kan Kwamishinan kuɗi na Jihar Bauchi, Dakta Yakubu Adamu, da wasu mutane bisa zargin tallafa wa ta’addanci da kuɗaɗen da yawansu ya kai Dala Miliyan 9.7 na Amurka.

Yakubu Adamu tare da Balarabe Abdullahi Ilelah, Aminu Mohammed Bose da Kabiru Yahaya Mohammed, waɗanda aka lissafta su a matsayin masu tuhuma na biyu zuwa na huɗu, za su gurfana a gaban Mai shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Laraba, bisa tuhume-tuhume guda 10.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa, duk da lauyan EFCC, Samuel Chime, ya roƙi kotu tun da farko da a bar Adamu da sauran waɗanda ake tuhuma su karɓi tuhumar a ranar da ake sauraron shari’ar da ke da alaƙa da wannan, Mai shari’a Nwite ya ɗage gurfanarwar zuwa ranar Laraba.

Alkalin ya bayyana cewa takardar ƙarar da ke ɗauke da lamba FHC/ABJ/CR/705/2025, wadda aka sanya hannu kuma aka shigar da ita a ranar 30 ga Disamba ta hannun Chime, ba ta cikin kundin shari’ar kotu a lokacin.

A tuhuma ta farko, an zargi Yakubu Adamu tare da Sirajo Jaja, wanda a lokacin shi ne babban akanta na Jihar Bauchi kuma yanzu yana gudun shari’a, da Samaila Irmiya Liman wanda shi ma yana gudun shari’a, da Balarabe Ilelah, Aminu Bose da Kabiru Mohammed, waɗanda dukkansu ma’aikatan gwamnati ne kuma masu sanya hannu kan asusun kuɗi ko takardun biyan kuɗin gwamnatin Jihar Bauchi, da aikata laifi a tsakanin watan Janairu zuwa Mayun 2024.

Karin karatu: Tinubu ya dage kan fara sabon tsarin haraji daga 1 ga Janairu duk da zargin sauya dokoki

An zarge su da haɗa kai wajen samar da kuɗaɗe da yawansu ya kai dala miliyan 2.3 na Amurka a tsabar kuɗi domin amfanin Bello Bodejo da mutanen da ke da alaƙa da shi, bisa amincewar da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayar, don yin amfani da waɗannan kuɗaɗen, gaba ɗaya ko wani ɓangare, wajen tallafa wa ɗan ta’adda ko ƙungiyar ta’addanci.

Laifin ya sabawa sashe na 26(1) kuma hukuncinsa na ƙarƙashin sashe na 21(2)(a) na Dokar Hana da Dakile Ta’addanci ta shekarar 2022.

A tuhuma ta uku, an zargi Adamu, Jaja da Liman waɗanda ke gudun shari’a, tare da Ilelah, Bose da Mohammed, da aikata laifi a tsakanin Janairu da Mayun 2024, inda ake zargin sun shiga wani tsari da ya kai ga isar da kusan dala 500,000 a tsabar kuɗi ga Bello Bodejo da mutanen da ke tare da shi domin manufar ta’addanci da kuma amfanin wata ƙungiyar ta’addanci da aka haramta, bisa amincewar da Gwamna Bala Mohammed ya bayar.

Wannan laifi ya sabawa sashe na 21(3)(b) kuma hukuncinsa na ƙarƙashin sashe na 21(4)(a) na Dokar Hana da Dakile Ta’addanci ta shekarar 2022.

A tuhuma ta huɗu, an zargi waɗanda ake tuhuma, ciki har da Jaja da Liman, da haɗa kai wajen ɓoye asalin kuɗaɗen dala miliyan 2.3 na Amurka, waɗanda kuɗaɗen gwamnatin Jihar Bauchi ne, ta hanyar masu canjin kuɗi na bayan fage da wasu wakilai, tare da mayar da su zuwa dala domin amfanin Bello Bodejo da mutanen da ke tare da shi, bisa amincewar da Gwamna Bala Mohammed ya bayar, alhali suna da hujjar sanin cewa kuɗaɗen sun samo asali ne daga wani haramtaccen aiki.

Laifin ya sabawa sashe na 21(a) kuma hukuncinsa na ƙarƙashin sashe na 18(3) na Dokar Hana da Dakile Wanke Kuɗi ta shekarar 2022.

A tuhuma ta takwas, an zargi waɗanda ake tuhuma, ciki har da Jaja da Liman, da haɗa kai a shekarar 2024 wajen ɓoye asalin kuɗaɗen kusan dala miliyan 6.95 na Amurka domin amfanin Yakubu Adamu, Kwamishinan kuɗi, waɗanda ake zargin sun fito daga haramtaccen aiki, kuma an ratsa da su daga kuɗaɗen gwamnatin Jihar Bauchi ta hannun masu canjin kuɗi na bayan fage.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya kuma rawaito cewa Bello Bodejo shi ne shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore.

Mai shari’a Nwite, a cikin wata ƙara ta baya da ta shafi zargin badaƙalar kuɗi na naira biliyan 4.6, ya bayar da umarnin tsare Yakubu Adamu a gidan tsare na EFCC har zuwa lokacin da za a gurfanar da shi tare da sauran waɗanda ake tuhuma a ranar Laraba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here