Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya ce gwamnati za ta duba duk wasu hanyoyin da za a bi domin tunkarar Majalisar Dokoki ta kasa na kin sake duba dokar zabe ta 2022.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan kudirin dokar a ranar 25 ga watan Fabrairu, ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta sake duba sashe na 84(12) na dokar, inda ya ce tanade-tanaden ya saba da na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka gyara).
Sai dai da yake amsa tambayoyin manema labarai na fadar gwamnatin tarayya bayan kammala taron majalisar zartarwa ta kasa (FEC) na wannan makon wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.
Malami ya ce har yanzu gwamnatin ba ta dauki wani matsayi ba kan kin sake duba dokar da majalisar dokokin kasar ta yi.
Ya ce gwamnati na da zabi uku da ta tanada bayan Majalisar Dokoki ta kasa ta ki amincewa da bukatar Shugaban kasa da suka hada da sake neman a sake nazari, tunkarar kotu ko kuma ta amince da doka yadda take.
Malami ya tabbatar da cewa, duk da cewa hakkin ‘yan majalisa ne su kafa doka, idan har ya zama dole, gwamnatin tarayya za ta yi amfani da dukkan hanyoyin da ta dace.
Sai dai ya ci gaba da cewa har yanzu gwamnati ba ta dau matsaya kan matakin da za ta dauka kan lamarin.
Shima da yake magana akan bukatar mikawa DCP Abba Kyari da gwamnatin Amurka tayi, Malami ya koka da cewa an tafka kuskure akan lamarin, yana mai cewa har yanzu ana kan aiwatar da bukatar.
Ya yi nadamar abin da ya kira rashin fahimtar da kafafen yada labarai suka haifar a kan lamarin, inda ya bukace su da su damke gaskiyar lamarin don kaucewa haifar da rudani.













































