Gwamna Yusuf ya ziyarci Shettima don taya shi murna kan zaben shi a matsayin mataimakin Tinubu

IMG 20260711 WA0185 750x430

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyarar girmamawa ga mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, bayan zabensa a matsayin abokin takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027.

Wannan na cikin wata sanarwa da Daraktan yada labaran Gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar.

A yayin ziyarar da gwamnan ya kai a daren ranar Juma’a a Gidan Aguda da ke Fadar Shugaban Kasa, Abuja, Gwamna Yusuf ya taya Mataimakin Shugaban Kasar murna bisa zabensa, inda ya bayyana hakan a matsayin amincewa da jajircewar da hidimarsa ga kasa.

Gwamnan ya yi addu’a Allah da ya ba Shugaba Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa Shettima hikima, lafiya da nasara yayin da suke shirin fuskantar zaben 2027.

A yayin ziyarar, gwamnan na tare da Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Gwale, Hon. Engr. Garba Diso, Hon. Muhammad Jamu Yusuf, Kwamishinan Harkokin Addini na Jihar Kano da Sheikh Ahmad Tijjani Auwalu.
Gwamnan ya sake jaddada goyon bayansa ga dukkan kokarin da ake yi na inganta hadin kai, zaman lafiya da cigaba mai dorewa a fadin Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here