Rundunar ƴan sandan Najeriya ta bayyana cewa har yanzu ba ta samu takardar umarnin kotun tarayya da ta dakatar da aiwatar da bada lasisin baƙin gilashin mota ba.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana haka a ranar Asabar yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa kotu ta hana rundunar kama ko gurfanar da masu mota saboda baƙin gilashin mota.
A tun farko, kotun tarayya ta Warri a jihar Delta ta bayar da umarni a shari’ar da ake yi da lamba FHC/WR/CS/103/2025 tsakanin John Aikpokpo-Martins da Sufeto Janar na ƴan sanda da kuma rundunar ƴan sanda ta Najeriya, inda ta umurci rundunar da ta dakatar da aiwatar da tsarin bada lasisin har sai an kammala shari’ar gaba ɗaya.
Labari mai alaƙa: Kotu ta umarci ‘yan sanda su dakatar da bada lasisin sanya baƙin gilashin mota
Kotun ta kuma bukaci rundunar ƴan sanda da ta ci gaba da bin matsayin da ake ciki a yanzu, wato kada ta ɗauki wani mataki kan masu baƙin gilashin mota har sai an yanke hukunci na ƙarshe.
Wannan karin bayani na rundunar ya zo ne bayan wani lauya mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, Inibehe Effiong, ya yada wani ɓangare na hukuncin kotu da ke hana ƴan sanda aiwatar da tsarin lasisin.
A watan Afrilu 2023 ne rundunar ƴan sanda ta sanar da dawo da tsarin samun lasisin baƙin gilashin mota bayan ta dakatar da shi a shekarar 2022.













































