Babbar kotun tarayya da ke zaune a Warri, jihar Delta, a ranar Juma’a ta bayar da umarni ga rundunar ‘yan sanda ta Najeriya da Sufeto Janar na ‘yan sanda da su dakatar da aiwatar da bada lasisin sanya baƙin gilashin mota.
Kotun ta umurce su da su ci gaba da bin doka tare da mutunta tsarin shari’a har sai an kammala sauraron shari’ar da aka shigar, mai lamba FHC/WR/CS/103/2025, wadda lauya John Aikpokpo-Martins ya shigar kan sahihancin wannan mataki.
Aikpokpo-Martins ya kalubalanci tsarin tilasta lasisin gilashin mota mai duhu a kotu, inda lauya Kunle Edun (SAN) ya jagoranci tawagar shari’ar.
Edun ya bayyana wa manema labarai cewa wannan matakin na kotu yana da muhimminci kuma ci gaba ne wajen tabbatar da bin doka yayin da ake jiran hukunci kan ainihin batun.
A watan Afrilu da ya gabata ne rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta sanar da dawo da tsarin bayar da lasisin gilashin mota mai duhu, bayan da ta dakatar da shi a shekarar 2022.
Wannan mataki ya jawo suka daga masu motoci da kungiyoyin kare hakkin dan Adam, inda aka ce tsarin na haifar da cin zarafi da karbar rashawa a wuraren bincike.
Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya sanya ranar 12 ga watan Agusta a matsayin wa’adin karshe ga masu motoci don samun lasisin, kafin daga baya ya kara wa’adin zuwa 2 ga watan Oktoba.
Rundunar ta kare tsarin, tana danganta shi da dokar hana amfani da baƙin gilashin mota ta shekarar 1991 da kuma batutuwan tsaro.
Sai dai masu kare hakkin dan Adam sun bayyana shi a matsayin sabawa kundin tsarin mulki da kuma hanyar cin moriyar masu motoci.
A makon da ya gabata, rundunar ‘yan sanda ta jihar Delta ta sanar da cewa za ta fara cikakken aiwatar da dokar hana amfani da baƙin gilashin mota daga ranar Alhamis 2 ga watan Oktoba, 2025, tare da daukar alkawarin gudanar da aikin cikin ladabi da mutunta hakkin ‘yan kasa.
Kotun ta ce dole ne rundunar ta dakatar da aiwatar da tsarin har sai an yanke hukunci a shari’ar.
NAN













































