Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Sunny Echono a matsayin sabon babban sakataren hukumar kula da manyan makarantu ta kasa (TETFund).
Mista Ben Goong, Daraktan yada labarai da hulda da jama’a a ma’aikatar ilimi ta tarayya ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Juma’a.
Goong ya bayyana cewa Echono ya karbi ragamar mulki daga hannun Farfesa Sulaiman Bogoro wanda wa’adinsa na shekaru biyar zai kare a ranar 18 ga Maris.
Tun da farko tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya nada Bogoro a watan Afrilun 2014, aka maye gurbinsa da wani, inda daga bisanu aka sake nada shi.
Goong ya bayyana Echono a matsayin ƙwararren masanin fasaha wanda zai yi amfani da kwarewar sa kawo wa kawo ci gaba a hukumar.
Kafin nadin nasa, Echono ya kasance babban sakataren ma’aikatar ilimi ta tarayya kuma mamba a kwamitin amintattu na TETfund
Ya yi karatun digiri na farko a fannin gine-gine a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, a shekarar 1983, inda ya yi digiri na biyu a fannin gine-gine, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, a shekarar 1985, inda ya yi Diploma a fannin Gudanarwa daga Jami’ar Calabar.
Har ila yau, yana da digiri na biyu a fannin sarrafa kayayyaki daga Jami’ar Turin, Italiya, da dai sauransu.













































