An gurfanar da wani basaraken kabilar Igbo wanda ya lashi takobin gayyatar kungiyar ta’addanci ta IPOB zuwa a Jihar Legas.
A yayin da yake barazanar gayyatar IPOB domin kare dukiyoyin ’yan kabilar Igbo a Legas, Nwagu ya ce kungiyar za ta koya wa mutanen jihar hankali.
Sai dai Nwagu, wanda shi ne tsohon shugaban ’yan kabilar Igbo da ke rukunin gidaje na Ajao da ke jihar, ya musanta zargin.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Y. A Adesanya ya dage sauraron karar zuwa ranar 4 da kuma 5 ga watan Yuni, 2023.












































