Gwamna Namadi ya jaddada aniyarsa ta bunkasa Ilimi da Lafiya a Jihar Jigawa

Umar Namadi
Umar Namadi

Gwamnan Jihar jigawa Malam Umar Namadi, ya jaddada aniyarsa ta bunkasa bangarorin ilimi da noma da kiwon lafiya tare da samar da ayyukan yi a jihar.

Ya bayyana hakan ne a sakon san a barka da sabuwar shekara ta 2024 ga al’ummar Jihar.

Yace a sabuwar shekarar nan gwamnatin sa za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan raya kasa da faro a shekarar da ta gabata ta 2023.

Karanta wannan: Kano: Gwamna Abba da mataimakinsa sun gudanar da bikin sabuwar shekara ta 2024

Ya kara da cewa kudurorinsa 12 sun fi mayar da hankali ne kan harkokin ilimi, lafiya, noma, gine-ginen hanyoyi da kuma samar da ayyukan yi.

Ya kuma yaba da irin kwazo da basirar da matasan jihar ke da ita, ta yadda zasu iya taimkawa sabuwar duniyar ta yi gogayya da sauran jihohin kasar nan.

Namadi ya bayyana ilimi a matsayin ginshikin ci gaban ko wacce al’umma, inda ya yi alkawarin rubanya kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen ganin an saukakawa jama’a musamman a harkokin kiwon lafiya.

Namadi ya yabawa al’ummar jihar bisa jajircewar da suka nuna wanda a cewarsa hakan ya sanya jihar shiga sabuwar shekara da kyakkyawan fata.

Karanta wannan: Tsoffin daliban BUK sun karrama Farfesa Mahmud Lawan da Farfesa Habu Fagge

Ya nuna matukar gamsuwa da irin hadin kan da al’ummar jihar ke da shi, duk da kalubalen zamantakewa da tattalin arziki da aka fuskanta a shekarar da ta gabata.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su hada kai, domin shawo kan matsalolin da ake fuskanta da kuma samar da kyakkyawar makoma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here