Gwamnan Kano Abba Kabir da mataimakinsa Aminu Abdussalam da sauran manyan jami’an gwamnati sun gudanar da bikin sabuwar shekara ta 2024.
Bikin da dimbin jama’a da suka halarta ya gudana ne a harabar filin Mahaha da ke cikin birnin Kano a karshen shekarar da ta gabata.
Gwamna Abba yace dole a yabawa al’ummar Kano la’akari da yadda suka zabi jam’iyyar NNPP ashekarar 2023 domin gudanar da al’amuran jihar tare.
Yace a shekarar 2024 da aka shigo za’a yi manya-manyan ayyukan ci gaban al’ummar kano tare da yada ribar dimokuradiyya a lungu da sako na Jihar.
Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta kammala gine-gine a rukunin filin wasanni na Mahaha don zama cibiyar matasa.
Karanta wannan: Gwamna Namadi ya jaddada aniyarsa ta bunkasa Ilimi da Lafiya a Jihar Jigawa
Acewarsa hatta tarukan jama’a da na addini da harkokin wasanni duk za’a rinka gudanarwa a filin.
Gwamnan ya jaddada aniyarsa wajen bunkasa harkokin wasanni domin hada kan matasan jihar da sauran bangarori domin zamantakewa da tattalin arzikin jihar cikin gaggawa.













































