Majalisar Dattawa ta amince da nadin tsohon babban hafsan tsaro Christopher Musa a matsayin sabon ministan tsaro.
Amincewar na zuwa ne bayan tantancewar da ta dauki sa’o’i biyar a zauren majalisar, kwana guda bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar da sunansa domin rike wannan mukami.
Nadin nasa ya zo ne a wani lokaci da matsalolin tsaro ke karuwa a Najeriya, musamman yawaitar garkuwa da mutane a makarantu.
Daya daga cikin manyan hare-haren da suka faru kwanan nan shi ne sace dalibai 25 a garin Maga na jihar Kebbi, inda rahotanni suka nuna cewa dakarun tsaro sun bar yankin kafin mahara su kai harin.
Labari mai alaƙa: Yanzu-yanzu: Tinubu ya nemi majalisa ta amince ya naɗa Christopher Musa a matsayin ministan tsaron Najeriya
A jawabinsa, Musa ya bayyana cewa abu na farko da zai yi shi ne binciko dalilan janye dakarun, yana mai jaddada cewa rundunar soji ba ta da al’adar gudu ko tsoro.
Ya ce za su bi diddigin lamarin tare da hadin kai da sauran hukumomin tsaro da ma’aikatun gwamnati domin kawo karshen matsalolin da ake fuskanta.
Ya ce dakarun soji suna da tsarin gudanar da ayyuka, kuma ma’aikatar tsaro za ta ci gaba da sanya idanu kan dukkan matakan da hukumomin tsaro suke dauka domin tabbatar da tsaron al’umma.
Cikakken bayani na nan tafe…..













































