Ofishin yada labarai na dakatacciyar sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ya ce ziyarar da ta shirya zuwa yankin Kogi ta tsakiya za ta yi tane domin gudanar da bikin Eid-el-Fitr zai gudana kamar yadda aka tsara.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, kungiyar ‘yan jarida ta Sanatan ta yi watsi da rade-radin da ake yi na yiwuwar soke ziyarar.
Tawagar ta bayyana cewa ofishinta bai bayar da wannan sanarwar ba, don haka ta bukaci jama’a da su yi watsi da wannan jita-jita.
“Mun yi farin cikin tabbatar da cewa ziyarar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta Sallah a gundumar Kogi ta tsakiya za ta ci gaba kamar yadda aka tsara,” in ji sanarwar.
Akpoti-Uduaghan ta jaddada kudirinta na yin cudanya da al’ummar mazabarta tare da inganta hadin kai a yankin majalisar dattawa.
Karanta: An aika wa Sanata Natasha wasiƙar da ƴan mazaɓarta suka tura na neman yi mata kiranye
Tawagar Sanatan ta kuma bayar da tabbacin cewa, an yi dukkan shirye-shiryen da suka dace don ganin an gudanar da bukukuwan cikin kwanciyar hankali da walwala.
Bayanin na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa gwamnatin jihar Kogi na yunkurin hana Akpoti-Uduaghan ziyartan mazabarta.
A ranar Litinin, gwamnatin jihar ta ba da sanarwar hana tarukan jama’a, saboda rahoton kalubalen tsaro da aka samu.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar Kingsley Fanwo ya fitar, ya ce an dauki matakin ne domin kaucewa duk wata barazanar tsaro da ka iya kawo tabarbarewar zaman lafiya a jihar.