NDLEA ta kama mata 4 da ake zargi da safar miyagun kwayoyi a jihohi 4

NDLEA 1 (1)

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ta kama mata 4 da ake zargi da safar miyagun kwayoyi a Jihohin Edo, Imo, Kano da Gombe.

Daraktan yada labarai da wayar da kai na Hukumar, Mr Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi a Abuja.

Ya bayar da cikakken bayani, inda ya ce an gudanar da wani aiki a Jihar Edowani, wanda jami’an NDLEA suka yi a wuraren da ake sayar da miyagun kwayoyi a cikin Birnin Benin a ranar 2 ga Yuni, inda ya kai ga kama manyan masu safar kwayoyi 4, ciki har da mata 3.

“A Uyosa, Birnin Benin, an kama mata 2 da wani haramtattun abubuwa ciki har da skunk gram 176, Loud gram 65, da Methamphetamine gram 5.” In ji sanarwar.

Ta kuma kara da cewa, a kan hanyar Agbor da ke Birnin Benin, an kama wata mata mai shekara 21 mai suna Anita Abraham da Scottish Loud gram 95 da regular Loud gram 329.

Haka zalika, a Upper Mission, Birnin Benin, an kama wani namiji da nau’ikan kwayoyi masu kawar da hankali daban-daban da suka hada da Loud, Colorado, Swinol, da Methamphetamine.

“A wani samamen na gaggawa da jami’ai suka gudanar a Jihar Kano ranar Alhamis, 4 ga Yuni, ya kai ga kama wani matashi mai suna Saifullahi Lawan mai shekara 19 a yankin Kafi na Madobi, da ganga 40 na skunk mai nauyin kilo 38.

A wani ci gaban mai alaka da wannan, Daraktan ya ce, jami’ai a Jihar Gombe ranar 1 ga Yuni sun kama wani mai shekara 28 kusa da Dantiti Plaza a yankin Tumfure na Gombe.“An kama shi da kwayoyin tramadol 15,000,” in ji shi.

Ya ce ayyukan wayar da kan jama’a na Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi (WADA) da NDLEA ke gudanarwa a duk fadin kasar ma ya ci gaba a makon da ya gabata.

Da yake mayar da martani kan jerin ayyukan da suka yi nasara, Shugaban hukumar ta NDLEA, Janar Buba Marwa (mai ritaya) ya yaba wa jami’ai maza da mata na rundunonin Imo, Edo, Kano da Gombe saboda juriya da faɗakarwarsu.

Marwa ya kuma yaba wa abokan aikinsu a duk rundunonin da ke fadin kasar saboda daidaita kokarinsu na rage ta’ammali da kwayoyi da rage bukatar kwayoyi.

Ya sake jaddada cewa hukumar ta himmatu wajen rusa hanyoyin safar kwayoyi kuma za ta ci gaba da kai samame kan masu safar kwayoyi ba tare da la’akari da shekaru, jinsi, ko hanyoyin boye kwayoyin ba. NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here