An yi ɗauki ɗora a jam’iyyarmu ta NNPP- Khaleed Shettima

images 1
images 1

Assalamu Alaikum Warahmatullahi ta’ala wabarakatuhu.
Kamar yadda aka sani an yi ɗauki ɗora a cikin jam’iyyarmu ta NNPP a dukkanin ƙananan hukumomin Kano 44 wajen fidda ƴan takara kama daga malisar jiha zuwa ta wakilai da sauransu. Ni ina cikin waɗanda Allah yasa suka nemi takarar majalisar ƙasa Allah bai sa na samu ba cikin ƙudurarsa aka zaɓi Hon Idris Dan Kawu wanda tuni na taya shi murna tare da yi masa fatan alkhairi.

Tun daga wannan lokaci babu wani cikin jagorori da banyi ƙoƙarin taɓa alli da shi ba amma babu wanda na samu ji daga gareshi a cikinsu ballan tana na san ta inda za’a ɗora domin na ci gaba da bada gudunmuwa fiye ma da wadda na bayar a baya domin kai wa ga nasara, in banda ta ɓangaren madugu Kwankwaso wanda ni kuma nake da saɓanin ra’ayin akan abinda na ji daga gareshi.

Tun daga wannan lokaci zuwa yau nake ta lallashi dimbin masoya akan su yi haƙuri a bar maganar takara amman matsin lambarsu ya sa ala-tilas na fara sauraron su domin jin matakin da suke so na ɗauka.

Ban shiga siyasa domin na taɓa muhibbar kowa ba, wannan tasa ba zan yi tambihi a kan abubuwan da suka faru da ni ba, Wanda ni na yarda da cewar faruwarsu karara cin amana ta ce! Dama tun farkon kaddamar da takarar nan tawa na fara ne da neman zaɓin Allah mafi Alkhairi.

A don haka muna wa Allah kyakkaywan zaton cewar jam’iyyar PRP ta Margayi Malam Aminu Kano mai alamar ɗan mukulli zata zamo jirgin fiton al’ummar Kano a 2023 inshaAllah..

Ku zo mu hadu domin mu yi dakonmu ƴan uwa!
Akwai saƙo nan gaba kaɗan insha Allah….

SHARHI 1

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here