Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta kama tsohon Gwamna Abdulaziz Yari kan binciken da hukumar ke yi akan dakataccen Akanta Janar na Tarayyar Najeriya Ahmed Idris.
Yari, wanda tsohon gwamnan jihar Zamfara ne an kama shi ne ranar Lahadi a gidansa da ke Abuja kwanaki kadan bayan ya lashe tikitin takarar Sanatan Zamfara ta yamma a jam’iyyar APC.
Tun a ranar 16 ga watan Mayu ne hukumar ta fara bincikar Ahmad Idris, kan zargin almundahanar kudin da ya kai Naira biliyan 80.
Abdul’aziz Yari, dai guda ne daga cikin wadanda ake zargi da hada bakin, wanda aka kama shi a ranar Lahadi 29 ga watan Mayun 2022 kamar yadda majiyar EFCC ta shaidawa Jaridar PREMIUM TIMES.
A cewar majiyoyin, ana zargin Yari da Dakataccen Akanta Janar din sun yi hada-hadar kudin tsakaninsu “daya kai Naira biliyan 20″.













































