Majalisar Dattawa Ta Amince Da Bukatar Tinubu Na Ciyo Bashin Dala Biliyan 2.2

Senate 1 750x430

A ranar Alhamis ne Majalisar Dattawa ta amince da bukatar shugaban kasa Bola Tinubu na lamunin dala biliyan 2.2 don yin wani bangare na gibin kasafin kudin shekarar 2024 na Naira tiriliyan 9.7.

Amincewar ta biyo bayan gabatar da rahoton da shugaban kwamitin majalisar dattawa akan basukan gida da waje, Aliyu Wamakko, ya gabatar yayin zaman majalisar.

Da yake jagorantar zaman majalisar, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya yabawa kwamitin bisa gaggawar da suka yi da kuma yin nazari sosai kan bukatar lamuni.

A cikin wata wasika da aka karanta yayin zaman majalisar dattawa da ta wakilai a ranar Talata, Tinubu ya bayyana cewa rancen na da muhimmanci ga dabarun kasafin kudin gwamnatin sa na shekara mai zuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here