Kungiyar KCSF  ta dakatar da Ibrahim Waiya, CDE

Ibrahim Waiya

Kungiyar farar hula ta Kano (KCSF) ta dakatar da  Malam Ibrahim Waiya da kungiyarsa ta Citizens for Development and Education (CDE), daga zama membobi da ayyukanta na tsawon shekara daya, daga ranar 20 ga Nuwamba, 2024.

Wasikar dakatarwar da Hamisu Isa Sharifai, sakataren kwamitin amintattu na KCSF ya sanya wa hannu ta fito ga manema labarai a Kano, ranar Laraba.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito wannan lamari na zuwa ne kwana guda bayan wata babbar kotun jihar Kano, karkashin jagorancin Hon. Mai shari’a Usman Mallam Na’abba, ya yi watsi da karar da Malam Waiya ya shigar a kan KCSF, inda ya tabbatar da sahihancin zaben da aka gudanar a ranar 8 ga watan Yuni, 2024.

A cikin wasikar, kungiyar bayyana rashin da’a da ayyukan da ya ke da nufin kawo cikas ga hadin kai a matsayin dalilan da suka sa aka yanke wannan hukunci.

BoT ya ce dakatarwar ta biyo bayan kin amsa gayyatar da Waiya ta yi masa tun farko a ranar 27 ga Yuli, 2024, don magance korafe-korafen rashin da’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here