Nigeria ta sake komawa matsayi na farko cikin jerim kasashen da suka fi samar da man fetur a Africa, biyo bayan fara samar da gangar mai fiye da miliyan daya a rana tun daga watan Nuwamba zuwa yanzu.
Kungiyar kasashe masu arzikin Man Fetur ta duniya OPEC ce ta sanar da haka cikin rahoton hada-hadar man fetur da ta fitar na watan Disamba.
Rahoton ya bayyana cewa an samu Nigeria ta samu kari kan yadda ta saba samarwa, inda aka samu karin fiye da ganga dubu 47 daga watan Octoba zuwa Disamba.
A rahoton da aka fitar a watan Octoba kasar Libya ce a matakin farko, sai dai tun daga lokacin ta samu koma baya na adadin gangar mai da take fitarwa musamman ma a watan Nuwamba, wanda hakan ya bawa Nigeria damar darewa mataki na farko.
Rahoton na OPEC ya kara da cewa kasar Saudiya da Iraq da Nigeria sune kasashen da suke kan gaba wajen samar da mai yayin da Angola da Libya Congo sune koma baya.
Rahoton ya kara da cewa an samu ci gaba kan farashin man fetur a wasu kasashe wanda hakan ya temaka wajen bunkasar tattalin arziki.













































