Gwamnatin Kano ta kaddamar da ingantaccen dakin gwaje-gwaje na sarrafa gurbatar yanayi

1000305511 scaled 1 750x430

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da dakin gwaje-gwajen yaki da gurbatar yanayi da aka gyara tare da inganta shi, wanda yake a Farm Center, a wani bangare na kudirinta na magance kalubalen muhalli da inganta lafiyar al’umma a jihar.

Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwar a ranar Larabar da ta gabata, kwamishinan muhalli da sauyin yanayi, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya bayyana cewa inganta aikin zai magance dogon bukatu na inganta ayyukan dakin gwaje-gwaje.

A cewarsa, tsawon shekaru, dakin gwaje-gwajen ya yi aiki a jihohin Kano, Kaduna, Katsina, Jigawa, Kebbi, Sokoto, da Zamfara, a matsayin dakin gwaje-gwajen muhalli daya tilo a yankin, a don haka gyare-gyaren yana da mahimmanci don daukaka matsayinsa zuwa matakin kasa da kasa.

“An kafa sashen kula da gurbatar yanayi shekaru ashirin da suka gabata, a karkashin ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi, an kirkiro shi ne biyo bayan kafa ma’aikatar muhalli ta tarayya a shekarar 1999. Babban aikin dakin gwaje-gwajen shine tabbatar da yanayi mai aminci da lafiya ta hanyar nazarin muhalli mai inganci. Yana taka muhimmiyar rawa wajen tantance yanayin jihar Kano da kuma sanya ido kan yanayin muhalli a cikin jihar Kano da kuma sa ido kan ka’idojin muhalli da na kasa da kasa. yana ba da mahimman bayanai don ingantaccen sarrafa muhalli.”

Kwamishinan ya yabawa gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa goyon bayan da yake baiwa wannan shiri.

WhatsApp Image 2025 04 09 at 19.15.44 1

Ya kuma gode wa ma’aikatan ma’aikatar, da kamfanin bayar da kwangila, da kwamitin sa ido kan gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar aikin.

Tun da farko, Daraktan hana gurbatar muhalli, Malam Ibrahim Nasir, ya yaba da kokarin ma’aikatar tare da bayyana alfanun da gyare-gyaren ke da shi ga lafiyar al’umma da kare muhalli.

Ya ce ginin da aka inganta a yanzu ya fi kyau don taimakawa wajen sa ido tare da magance matsalolin muhalli a fadin Kano da jihohi makwabta.

A nata jawabin shugabar dakin gwaje-gwajen, Dakta Amina Muhammad Ibrahim, ta bayyana jin dadin ta ga kwamishinan da gwamnan jihar Kano bisa wannan gyara, inda ta bayyana aikin a matsayin wanda ya dace kuma abin a yaba ne.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here