Gwamna Yusuf ya yaba wa matsahin kwamishina Dahir Hashim kan kwazosa

IMG 20260530 WA0202 750x430

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa kwamishinan muhalli, Dr. Dahir Muhammad Hashim, inda ya bayyana shi a matsayin mai samar da ci gaba da kwazo duk da kasancewarsa mafi karancin shekaru cikin kunshin kwamishinoni a majalisar zartarwa.

Gwamna Yusuf ya yaba da jajircewar Dr. Hashim, samar da abubuwa da kuma kwazonsa wajen karfafa ayyukan gwamnati da karfafa sadarwa tsakanin gwamnati da jama’a.

Jawabin Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a.

A cewar sanarwar, gwamnan ya yi gargadi mai karfi ga kwamishinoni da masu ba shi shawara na siyasa a gwamnatinsa, inda ya jawo hankalinsu su tabbatar sun cancanci amincewar da aka ba su ta hanyar ingantaccen aiki da himma wajen mulki.

Gwamna Yusuf ya yi wannan yabo da gargadi ne a jawabin da yayi a bikin Hawan Nasarawa na Sallah da aka gudanar a Kano.

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci sakaci, rashin aiki ko rashin himma daga kowane mai mukami ba, yana mai cewa auna sakamakon masu rike da mukamai ginshikin ne a gwamnatinsa.

Ya roki mambobin Majalisar Zartarwar Jiha da masu ba shi shawara na siyasa da su ci gaba da sadaukar da kansu wajen hidima wa al’umma da goyon bayan tsare-tsaren ci gaba na gwamnati.

Gwamna Yusuf ya ce duk wani mai mukami da ya kasa aiki kamar yadda ake sa rai, ko dai ya inganta ko kuma ya shirya fita daga ofis.

Gwamnan ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen bayan ga duk sadaukarwa, kwarewa da nagarta a hidimar gwamnati.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here