Gwamna Nasir El Rufa’i na jihar Kaduna, ya ce tare da kyakkyawar manufa, ana iya zabe ta hanyar amfani da na’urorin zamani a Najeriya.
A cewarsa, nasarorin da aka samu a zaben kananan hukumomin jihar da aka kammala, wanda aka yi amfani da na’ura mai kwakwalwa, ya tabbatar da cewa ana iya ci gaba da hakan a fadin kasar nan.
Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wani shiri na musamman da aka yada a fadin jihar a jiya laraba, domin godewa al’umar jihar bisa zaben jam’iyyar APC da suka yi.
Ya bayyana zaben a matsayin wani al’amari da ya sake tabbatar da hadin kan jihar, yana mai cewa sakamakon zaben na yankin Kudancin Kaduna kadai, manuniya ce cewa za a iya magance raba-raben kawuna tsakanin bangarorin jihar.
A cewar sa, gwamnatin sa ta dora sahihancin zaben sama da komai, sabanin al’adar cinye du ta gwamnatocin da suka gabata.
Daga nan sai ya yabawa masu zabe a jihar da suka tabbatar wa duniya a karo na biyu cewa, amfani da na’urorin zamani wajen gudanar da zabe abu ne mai yiwuwa a Najeriya.
El-Rufai ya tunasar da cewa masu zabe a jihar sun kafa tarihi a ranar 12 ga watan Mayun 2018, lokacin da suka kada kuri’un su ta hanyar amfani da na’urar zamani domin zaben shugabanni da kansilolin su a fadin kananan hukumomi 23 da ke jihar ta Kaduna.
Ya kuma kara da cewa, da wannan nasara, Kaduna ta zamo jiha ta farko a fadin kasar nan da ta fara amfani da na’urar zamani wajen kada zuri’a kuma jiha ta farko a nahiyar Afrika.
Har ila yau, ya kuma bugi kirjin cewa, zaben ya sanya Najeriya a matsayin kasa ta farko a Africa bayan Namibia da aka yi amfani da irin fasahar.
“Zaben da aka gudanar na ranar 4 ga watan Satumbar 2021 ya sake tabbatar da aniyar gwamnatin jihar Kaduna wajen karkato da hankula dangane da amfani da na’urorin zamani domin inganta sahihancin zabe.
“Kaduna, karkashin jagorancin gwamnatin da bata dauki zabe a matsayin wani abu na ko a mutu ko ayi rai ba, ta bude sabon shafin ci gaban harkokin zabe a Najeriya ta hanyar amfani da na’urorin zamani”.
“A matsayina na gwamnan wannan jiha, ina da yakinin cewa, dukkan za mu yi nasara idan aka karfafa demukradiya.”
Ya kuma yi wa dukkan wadanda suka samu nasara a zaben murna tare da kalubalantar su da su yi amfani da damar da suka samu wajen bautawa al’umar su da kuma tabbatar da dorewar demukradiyya da zaman lafiya a jihar.
A gefe guda kuma, ya godewa al’umar jihar bisa goyon bayan da suka bawa jam’iyya mai mulki ta APC a zaben.
“Al’umar mu ta sake tabbatar da cewa tana yabawa da kokarin da muke yi wajen tallafa mata a bangaren abun da ya shafi ilimin ‘ya’yan su, samar da ingantattun hanyoyin kiwon lafiya da dai sauran su”.