Hukumar yaki da cin hanci da sauran laifuffuka ta kasa ICPC, ta ce tana shirin aika sammaci ga ‘yan kwangilar dake aikin ginin rukunin azuzuwa a makarantun firamaren Kwalli da Kofar Mazugal dake kananan hukumomin kwaryar birnin da Dala, biyo bayan rashin kammala ayyukan mazabu.
Babban mataimakin sufritanda na ofishin ICPC dake Kano, Bukar Galadima ne ya sahidawa Solacebase hakan a ranar Laraba, yayin aikin bibiyar ayyukan mazabu sanatocin yankunan tsakiya da arewacin jihar.

Solacebase ta ruwaito cewa, yayin ziyarar ayarin hukumar ICPC a makarantar firamare ta Kwalli dake yankin karamar hukumar birni da ta Kofar Mazugal dake karamar hukumar Dala, sun lura cewa ayyukan da aka yi tun na kasafin kudin shekarar 2020 ne.
Ta kuma ce “Fentin ya fara ɓarewa da sauran wasu Karin matsaloli.
“Ba su yi daidai da ka’idojin da kwangilar ta tanada ba, don haka hukumar ta shirya gayyatar ‘yan kwangilar game da aikin” a cewar ICPC.

Bukar Galadima yace ayarin hukumar ta lura cewa ginin rukunin ajujuwan a Kwalli da Kofar Mazugal, dake karkashin Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya ba su da kyau, inda rufin ke cikin wani hali mara kyau na yoyo, sannan ba bu kujeru da tebura.
Sarkin Kontagora Alhaji Sa’idu Namaska Ya Rasu
Har ila yau, yayin aikin bibiyar, ICPC ta yabawa Sanata mai wakiltar Kano ta arewa, game da yadda ya tsare gaskiya wajen aiwatar da aikin sanya fitilun titi masu amfani da hasken rana a garin Ganduje da Dawakin Tofa da Dambatta.
Idan za a iya tunawa, ICPC ta fara aiwatar da kashi na uku, na bibiyar yadda ake aiwatar da ayyukan mazabu ne a makon da ya gabata a jihohi 17, ciki har da Kano.
kuma kawo yanzu a Kano, hukumar ta ziyarci yankunan kananan hukumomin Kiru da Bebeji da Kura da Madobi da Garum Malam da Warawa da Dawakin Kudu.
Sauran sun hada da Dala da kwaryar birni da Dawakin Tofa da kuma Dambatta.













































