{HOTUNA}: Kano ta kaddamar da aikin farfado da madatsar ruwa ta Joda bayan shekaru bakwai bata aiki

images 66

Gwamnatin Jihar Kano ta fara aikin gyara a madatsar ruwan yanki ta Joda bayan wata ziyarar dubawa da ta kai wurin a makon da ya gabata, inda hukumomi suka ce an samu gagarumin ci gaba wajen maido da samar da ruwa ga al’ummomin da madatsar ke rarrabawa.

SolaceBase ta ruwaito cewa an bayyana hakan a wata sanarwa da Kwamishinan Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, Dr. Dahiru M. Hashim, ya sanya wa hannu da kan shi a ranar Talata.

Ya bayyana wannan mataki a matsayin mai matukar muhimmanci da tarihi, yana mai cewa wurin bai taba bayar da ko da lita guda na ruwa ba a cikin shekaru bakwai da suka gabata.

A cewar kwamishinan, an fara aikin gyara ne nan da nan bayan ziyar, wanda ta haifar da gyaran rijiyoyin bututu guda hudu, wadanda yanzu suna aiki suna kuma samar da ruwa ga manyan tankuna biyu na wurin da ke da karfin lita 720,000 gaba daya.

FB IMG 1782848309194 1536x1024 FB IMG 1782848317684 1536x1024

“Muna farin cikin sanar da ku cewa an fara aikin gyaran nan da nan bayan ziyar dubawa da muka kai, kuma an samu gagarumin ci gaba,” in ji Hashim.

Ya bayyana cewa an gyara daya daga cikin injinan samar da wutar lantarki na wurin cikin nasara, yayin da ake sa ran za a kammala gyaran dayan injin da maido da wutar lantarki ta babbar hanyar kafin ranar Laraba.

Kwamishinan ya kara da cewa an gyara biyu daga cikin kayan aikin hudu masu karfi na wurin, kuma suna aiki yanzu haka, yayin da injiniyoyi ke aiki don maido da sauran biyun.

Hashim ya ce gyaran zai bai wa madatsar, wanda ke da karfin samar da lita miliyan 9.6 na ruwa a kowace rana, damar sake tura ruwa zuwa al’ummomin da ke kan layin rarrabawarsa a cikin kwanaki masu zuwa.

FB IMG 1782848357446 1536x1025 FB IMG 1782848328912 1536x1025

Ya sake jaddada kudurin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na inganta samar da ruwan sha mai tsafta ga al’ummomin karkara a fadin jihar.

A cewar sa, Gwamna Yusuf ya ba da umarnin a gina karin rijiyoyin bututu da kuma cikakken gyaran ofisoshin gudanarwa na wurin da sauran muhimman kayayyakin more rayuwa domin tabbatar da cewa tsarin ya dawo cikakken aiki.

“Kokarin mu na hadin gwiwa yana haifar da sakamako na zahiri ga al’umma,” in ji kwamishinan, inda ya bayyana kyakkyawan fatan cewa wannan aikin da ake yi zai inganta samar da ruwa sosai a al’ummomin da abin ya shafa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here