Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dakatar da Shugaban Ma’aikatansa, Femi Gbajabiamila, kan zargin cewa ya karbi Naira miliyan 400 ta hannun wani, kuma ya sake nemi wata Naira miliyan 200 don saukake nadin Adeniyi Adeyemi a matsayin Darakta-Janar na Majalisar PFIPC.
A cikin wata sanarwa da kakakin Atiku, Paul Ibe, ya fitar a ranar Talata, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce dole ne Tinubu ya ba da misali ta hanyar hukunta mutanen da ya nada da kan shi.
Dan siyasar ya ce ikirarin shugaban ma’aikatan na cewa PFIPC ba hukumar gwamnati ba ce, ya kara raunata amincewa da gwamnati, ya kara nuna matsalolin gwamnatin.
“Ta yaya za ku ware Naira biliyan 27.4 a cikin kasafin kudi ga hukumar gwamnati wadda babu ita, ba tare da samar da tambayoyi da yawa ba,” in ji Atiku.
Ya lura cewa ware kudin jama’a ga hukumar da babu ita ya haifar da tambayoyi kan sahihancin dukkan kasafin kuind kasar na 2026.
“Ba za a iya boye wannan zargin zambar kasafin kudi ba da raunin bayanin da ba zai gamsar ba da shugaban ma’aikatan ya bayar,” in ji shi.
Dan takarar shugaban kasar ya bukaci Tinubu da ya dakatar da Gbajabiamila sannan ya ba da umarnin yin bincike mai zaman kansa don gano cikakkiyar gaskiya kan abin da ya bayyana a matsayin “mummunan abin kunya na kasa.”
Atiku ya ce, “Mulki mai kyau ya dogara ne kan gaskiya da rikon amana kuma ba za ka samu hakan ba ta hanyar kare iyalai da abokai.”
“Dole ne Shugaba Tinubu ya ba da misali ta hanyar hukunta shugaban ma’aikatansa daidai da ka’idojin rikon amana kamar sauran jami’an gwamnati. Naira biliyan 27 ba wasa ba ce.”
“Dole ne a yi aiki da doka a wannan lamari. Shugaba Tinubu ya nuna wa ‘yan Najeriya cewa akwai da gaskiya da rikon amana a gwamnatinsa,” in ji shi.
Da farko, Adeyemi ya yi zargi a wani taron manema labarai cewa Gbajabiamila ya nemi kashi 48 cikin 100 na kudin fara aikin PFIPC na Naira biliyan 27.4.
“Babban dalilin rashin jituwa tsakani na da shugaban ma’aikata shi ne cewa an zargin ya nemi kashi 48 cikin 100 na kudin fara aiki Naira biliyan 27,395,510,136 daga hukuma guda wadda ya musanta, wanda na ki, bayan ya karbi jimillar Naira miliyan 400 ta hannun wani, tare da sauran Naira miliyan 200 don tabbatar da nadin da ake magana a kai,” in ji Adeyemi.
Da yake martani kan zargin a ranar 11 ga Yuni, Gbajabiamila, a cikin wata sanarwa, ya nesanta kansa daga PFIPC kuma ya musanta sanin nadin Adeyemi a matsayin shugaban hukumar.
Gbajabiamila ya ce, “Ina sanar da jama’a da su lura cewa irin wannan ofishin ba na a wannan gwamnatin ba ne, kuma ba a yi wani nadi ba game da hakan.
“Ana ba ofisoshin diflomasiyya da na kasashen waje, cibiyoyin kudi da na kasa da kasa, kungiyoyin ci gaba, hukumomin tsaro da sauransu shawarar su lura da abin da ke cikin wannan sanarwa.”












































