INEC ta sanar da ranar gudanar da zabukan gwamnonin Ekiti da Osun

INEC Mahmood Yakubu 750x430

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta tsayar da ranar 20 ga watan Yuni da 8 ga watan Agustan 2026 a a matsayin ranar gudanar da zabukan gwamnonin Ekiti da Osun.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da haka a wajen rantsar da sabbin kwamishinonin zabe guda shida a shalkwatarta hukumar yau Juma’a a Abuja.

Ya ce, jadawalin ayyukan zabukan biyu hukumar ta amince da su ne bisa bin doka.

Yakubu ya ƙara da cewa bisa ga ka’idojin da doka ta tanada, INEC na da hakkin buga sanarwar manyan zabukan ne kasa da kwanaki 360 kafin ranar da aka kayyade.

Ya ce, a baya, an gudanar da zabukan gwamnoni a jihohin a watan Yuni da Yulin 2022, wa’adin mulkin gwamnonin biyu zai kare a shekarar 2026.

Yakubu ya kuma ce, a jihar Ekiti, za a gudanar da zaben ne a ranar Asabar, 20 ga watan Yunin shekerar 2026, yayin da za a fara zaben fidda gwani na jam’iyyar a ranar 20 ga Oktoba, kuma za a kammala a ranar 10 ga watan Nuwamba.

A cewarsa, wannan zai bai wa jam’iyyun siyasa damar sayar da fom din tsaya wa takara tare da kammala sayarwa duk a kan lokaci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here