Ƴan sanda sun cafke mutane 41 da ake zargi da hannu a kashe DPO na Rano

Police badge (1)

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta ce ta kama wasu mutane 41 da ake zargi da hannu a kisan Baturen ƴan sanda na Rano CSP Baba Ali.

Rundunar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da jami’inta na hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar yau Alhamis a madadin kwamishinan ‘yan sandan, Ibrahim Adamu Bakori.

Rundunar ta bayyana lamarin a matsayin wani mummunan hari kan jami’anta da kuma sadaukarwar jami’an ‘yan sanda da ke sadaukar rayuwarsu don kare al’umma.

A cewar sanarwar, kamen ya biyo bayan wani kwakkwaran bincike da aka gudanar, Yayin da rundunar ke yin iyakar kokarinta wajen cafke duk wadanda ke da hannu a kisan, da kuma aikata barna da kone-kone da ke da alaka da lamarin.

SolaceBase ta ruwaito cewa Kwamishina Bakori ya bai wa jama’a tabbacin cewa rundunar za ta jajirce wajen tabbatar da adalci da tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyi a fadin jihar.

Ya kuma bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da bai wa ‘yan sanda hadin kai a yayin gudanar da bincike.

Rundunar ta yaba da bajintar CSP Baba Ali da sauran jami’an da ke ci gaba da yi wa jihar Kano hidima da kwazo, inda ta sha alwashin cewa, za a gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kotu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here