Majalisar Dattawan Najeriya ta dage ranar da za ta koma zaman majalisa da makonni biyu, daga Talata, 23 ga Satumba, 2025 zuwa Talata, 7 ga Oktoba, 2025.
Majalisar ta dakatar da zaman ta tun ranar 24 ga Yuli, 2025 domin hutun shekara-shekara, kuma an zata za ta ci gaba da zama a yau Talata kafin wannan sauyi.
A cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikata na majalisar dattawa, Chinedu Akubueze, ya fitar ga ’yan majalisa, ya bayyana wannan jinkiri tare da neman afuwa kan duk wata matsala da hakan zai iya haifarwa.
Duk da haka, ba a bayar da cikakken dalili kan dagewar ba.
Sanarwar ta yi kira ga sanatoci da su lura da sabon jadawalin tare da daidaita shirye-shiryensu bisa ga sabon lokaci.
Haka kuma ta nuna cewa an yi wannan sauyi ne cikin gaggawa tare da neman fahimtar ’yan majalisa.
Abu mai jan hankali shi ne, wannan sanarwar ta fito daga ofishin shugaban ma’aikata na majalisar dattawa maimakon sakataren majalisar, wanda a al’ada shi ne kan fitar da irin wannan sanarwa.
A makon da ya gabata ne Hukumar Ayyukan Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da nada Emmanuel Odo a matsayin mai rikon mukamin sakataren majalisar dattawa.
An amince da nadin nasa ne ranar Talata, 16 ga Satumba, 2025 a wajen taron hukumar karo na goma.












































