Gwamnatin jihar Kebbi ta kori wasu hakimai 3 bisa zargin rashin da’a

Kebbi Gov. Nasir Idris 750x430

Gwamnatin jihar Kebbi ta sauke hakimai 3 a masarautar Gwandu, sakamakon samun su da aikata dabi’un da suka sha bambam da masarautar.

Da yake sanar da korar Hakiman ranar Alhamis a Birnin Kebbi, Shugaban Hukumar Kula da Ma’aikatan Kananan Hukumomi, Alhaji Mansur Shehu, ya shaida wa manema labarai cewa matakin ya yi daidai da dokokin da’ar ma’aikatan gwamnati (wato PSR) na jihar.

Karanta wannan: ‘Yan-kasuwa sun koka da yadda Jami’an tsaro a Kebbi ke karbar kudi a hannun su

Wadanda aka kora sun hada da Allhaji Lawal Yakubu, Mai Arewan Yeldu a karamar hukumar Arewa da Malam Ahmed Sani, Sarkin Gabas Geza a karamar hukumar Dandi da kuma Alhaji Tukur Aliyu, Jagwadejin Bakuwe a karamar hukumar Suru.

Shehu ya ce korar hakiman ta zama tilas ne bayan da hukumar kula da ma’aikata ta karamar hukumar ta yi bincike kan tuhume-tuhumen da kananan hukumominsu ke yi musu.

Karanta wannan: Gwamnatin Taraba ta haramta hawa babura a birnin Jalingo

Ya bayyana cewa babban mai shari’a ya lura da kowacce daga cikin shari’o’i uku da aka sanar a hukumance, za a ci gaba da bincike tare da bankado wasu karin hujjoji.

Shehu ya jaddada cewa bayan bincike da tuntuba hukumar ta samu hakiman da laifin rashin da’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here