
Wata ma’adina da ake hakar zinari ta bayan fage ta ruguje a karshen makon da ya gabata a kasar Mali, inda ta kashe mutane sama da 70, kamar yadda wani jami’i ya fada a ranar Laraba, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike bisa fargabar cewa adadin na iya karuwa.
Karim Berthé, wani babban jami’i a Hukumar kula da mu’adinan karkashin kasa da aikin hakar mu’adinai National Geology and Mining Directorate, ya tabbatar da cikakkun bayanai ga Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press kuma ya kira lamarin hadari.
Akwai kusan mutane 100 a cikin mahakar ma’adinan a lokacin rugujewar, a cewar Abdoulaye Pona, shugaban hukumar kula da ma’adinan kasar Mali, wanda ya je wurin.
Karanta wannan: Ƴan sanda sun kama matar da ta ajiye zaki a gidanta
Ana gudanar da bincike kan musabbabin rugujewar da ta faru a gundumar Kangaba da ke kudu maso yammacin yankin Koulikoro a ranar Juma’a. An fara ba da rahoto a ranar Talata a cikin wata sanarwa da ma’aikatar ma’adinai ta fitar da ta kiyasta cewa da yawa masu hakar ma’adinai sun mutu.
Irin wadannan bala’o’i sun zama ruwan dare a kasar Mali, wadda ita ce kasa ta uku da ke samar da zinari a Afirka. Masu aikin hakar kananan ma’adinai na yau da kullun ana zarginsu da yin watsi da matakan tsaro, musamman a wurare masu nisa.
Karanta wannan: Kotu ta yanke wa masu yunƙurin juyin mulki a Ghana hukuncin kisa
Bethe yace, “Dole ne jihar ta samar da tsari ga wannan fannin na hakar ma’adinai don guje wa irin wadannan hadarurruka a nan gaba,” in ji Berthe.
Sanarwar ma’aikatar ma’adinai ta yi matukar nadamar rugujewar, kuma ta bukaci masu hakar ma’adinai da al’ummomin da ke zaune kusa da wuraren hakar ma’adinai su kiyaye ka’idojin kariya.