Kotun daukaka kara ta sanya ranar da za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan Edo

OkpebholoIghodalo

A ranar Laraba ne kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Edo za ta yanke hukunci kan karar da jam’iyyar PDP da dan takararta, Asue Ighodalo suka shigar kan zaben gwamnan jihar Edo a ranar 21 ga Satumban 2024.

Jam’iyyar PDP da Ighodalo na kalubalantar matakin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dauka na ayyana Sanata Monday Okpebolo na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

Inda suka yi zargin cewa an tabka magudi a zaben.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa kotun mai mutane uku karkashin jagorancin mai shari’a Wilfred Kpochi, a ranar 3 ga watan Maris, ta ajiye hukunci a cikin karar bayan da bangarorin suka amince da adreshinsu na karshe a rubuce.

Kotun za ta yanke hukunci a cikin korafe-korafe uku masu alamar: EPT/ED/GOV/01/2024, EPT/ED/GOV/02/2024 da EPT/ED/GOV/03/2024.

NAN ta ruwaito cewa kotun ta fara sauraren karar ne a ranar 31 ga watan Janairu tare da shaidu 148 da kuma na’urar (BVAS) da aka yi amfani da su a yayin gudanar da zaben gwamna da ake takaddama a kai.

Wani babban jami’in fasaha a Sashen ICT na INEC, Anthony Itodo ne ya bayar da na’urorin, kuma kwamitin ya shigar da kara a gaban kotu.

Masu shigar da kara sun bukaci INEC da ta samar da na’urorin BVAS da aka yi amfani da su a rumfunan zabe 133 da ake ta cece-kuce kan sakamakon zabe.

Karin karatu: INEC ta sanar da karbar bukatar yiwa Natasha kiranye a majalisar dattawa

INEC ta bayyana cewa Okpebholo na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 291,667 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Ighodalo na jam’iyyar PDP, wanda ya samu kuri’u 247, 655.

Sakamakon rashin gamsuwa da sakamakon zaben, jam’iyyar PDP da dan takararta sun tunkari kotun, inda suka bukaci ta soke zaben da INEC ta bayyana APC da Okpebolo a matsayin wadanda suka lashe zaben.

Wadanda suka shigar da karar dai, sun ce zaben gwamnan bai yi nasara ba saboda zargin rashin bin dokar zabe ta 2022.

Sai dai jam’iyyar APC da Okpebholo sun bukaci kotun da ta yi watsi da kararrakin saboda rashin tushe balle makama, inda suka ce wadanda suka shigar da karar sun kasa tabbatar da zargin a cikin karar da suka shigar.(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here