Sanata Rabiu Kwankwaso ya mayar da martani kan barazanar marin sa da tsohon mataimakinsa kuma gwamnan jihar mai barin gado, Abdullahi Ganduje ya yi.
Kwankwaso ya ce ko kallon tsabar idonsa Ganduje ba ya iya yi, ba ma kallon banza ba, ballantana har ya iya karfin halin sa masa hannu.
A cewarsa, Ganduje ya riga ya rude ne a lokacin yake barazanar marin sa a Fadar Shugaban Kasa, inda Gandujen ya kai karar Gwamnan Kano mai ci, Abba Kabir Yusuf, kan rusau da yake yi a wuraren da gwamnatin Ganduje ta yi gine-gine ko ta sayar da filaye a jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa bayan ganawar Tinubu da Ganduje a ranar Juma’a da shugaban kasan ya gana da Kwankwaso a kan batun, Ganduje ya shaida wa ’yan jarida cewa da sun yi ido hudu da Kwankwaso da zai iya zabga tsohon uban gidan nasa mari.
Amma a martanin Kwankwaso ya ce, “Na ji cewa ( Ganduje) ya ce zai mare ni, to a ga ni nan. Ya rude ne kawai.
“Wadannan duk yarana ne a siyasance, ba sa iya kallona kai-tsaye idan muka hadu.
“A gigice yake a lokacin da ya fadi haka, amma dukkansu yarana ne ’yan siyasa wadanda idan sun gan ni sunkuyar da kansu suke yi,” in ji Kwankwaso.
A hirilarsa da BBC a safiyar Asabar, Kwankwaso ya bayyana cewa ya gana da Shugaba Tinubu na tsawon sa’o’i biyu a fadar shugaban kasa, kuma ya nasarar gamsar da shi kan badakalar filaye da sauran kura-kurai da gwamnatin Ganduje ta yi.
Ya kara da cewa bayan ya fede wa Tinubu biri har wutsiya, shugaban ya yi matukar mamakin abubuwan da ya bayyana masa kan badakalar filayen da Gwamnatin Ganduje ta yi a jihar.
Ya yi zargin cewa Ganduje ya yanka filayen filin sukuwa ya sayar wa ’yan uwa da abokan arzikinsa, lamarin da ya sa yanzu da kyar masu son motsa jiki a filin suke samu wuri.
A cewarsa, hatta filin sallar idi Ganduje bai kyale ba, sai da ya gina shaguna a kewayen filin, wanda a nan ne Sarkin Kano da sauran manyan baki suke halartar Sallar Idi.
Kwankwaso ya bayyana cewa akwai yiwuwar Tinubu zai shigar da wasu ’yan adawa a gwamnatinsa, kuma akwai yiwuwar zai iya samun muƙamin minista a gwamnatin.