Yanzu Emefiele na hannunmu – DSS

Godwin Emefiele
Godwin Emefiele

Hukumar tsaron farin kaya a Najeriya ta DSS ta ce yanzu haka ta kama tare da tsare tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele.

A safiyar yau Asabar DSS ta ce Emefiele ba ya hannunta a lokacin, kafin daga baya ta tabbatar da cewa ya shiga hannun nata a yanzu.

Tun a daren jiya Juma’a wasu rahotanni suka ce jami’an tsaron sun yi awon gaba da shi jim kaɗan bayan Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi daga muƙaminsa.

“DSS na tabbatar da cewa Emefiele, tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, yanzu haka yana hannunmu don gudanar da bincike,” a cewar wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu da jam’iyyarsa ta APC sun zargi Emefiele da yunƙurin hana su yin nasara a babban zaɓen da aka kammala a watan Fabrairu saboda tsarin rage yawan kudi a hannun jama’a da ya ƙaddamar da kuma sauya fasalin kudi na naira.

Kafin haka, DSS ta zargi Emefiele da taimaka wa ta’addanci, har ma aka kai shi kotu kan zarge-zargen.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here