Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa mai zaman kanta ta ƙasa ICPC ta shigar da tuhume-tuhume guda 10 kan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, a gaban Babbar Kotun Tarayya da kuma Babbar Kotun Jihar Kaduna.
Tuhume-tuhumen sun haɗa da zargin amfani da mukami ba daidai ba, damfara, cin amana, karya dokokin saye da bayar da kwangila, da kuma haɗin baki wajen aikata laifi.
A cewar hukumar, shari’ar da ke gaban Babbar Kotun Tarayya ta fi karkata kan zargin wanke kuɗi da karɓar kuɗaɗe da bai cancanta ba.
An shirya gurfanar da El-Rufai a gaban kotu ranar Talata a Kaduna.
Ana zarginsa da karɓar sama da Naira Miliyan 289 a matsayin kuɗin sallama daga aiki fiye da abin da doka ta tanada.
Haka kuma ana zargin ya karɓi wasu kuɗaɗe a ƙasashen waje da aka danganta da ayyukan da ba su dace ba.
ICPC ta bayyana cewa shari’ar da ke gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna ta ƙunshi wasu zarge-zarge da suka shafi bayar da kwangiloli, amfani da kuɗaɗen jama’a da kuma harkokin filaye a lokacin mulkinsa.
Daya daga cikin zarge-zargen shi ne kashe kimanin Naira Biliyan 11 a kan aikin layin dogo da aka bai wa wani kamfani da ba a yi masa rajista yadda ya kamata ba, kuma aikin bai taɓa kammala ba.
Hukumar ta kuma ce an karkatar da sama da dala Miliyan ɗaya daga cikin rancen Bankin Duniya ba bisa ƙa’ida ba. Haka kuma ana zargin ya amince da bayar da kwangilar CCTV ta Naira Biliyan 4.61 ga wani kamfani ba tare da bin dokokin saye da bayar da kwangila ba, tare da sake ba shi wata kwangila ta dala miliyan 22.475.Q
Bugu da ƙari, ana zargin El-Rufai da aikata damfara a harkar filaye da kuma ƙoƙarin hana gudanar da bincike.
Ana zargin cewa ya haɗa baki da wani mutum domin bayar da cin hanci a ciki da wajen ƙasa domin tasiri ga masu binciken gwamnatin tarayya. ICPC ta jaddada aniyar ta na tabbatar da gaskiya da adalci tare da roƙon jama’a su bar kotu ta yanke hukunci.













































