A ranar Alhamis ne kwamitin da gwamnatin jihar Kano ta kafa ya tafi domin gudanar da bincike kan kisan da aka yi wa wasu matafiya Kano 16 da aka kona kurmus a garin Uromi na jihar Edo.
Wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin gwamnan jihar Kano, Ibrahim Garba Shu’aibu ya fitar ce ta bayyana hakan, inda ta kara da cewa wannan tafiya na da nufin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Sanarwar ta ce an kafa kwamitin ne saboda nuna damuwa da al’ummar kasar nan suka nuna dangane da munanan hare-hare da ake kaiwa a cikin al’umma, wanda ya yi sanadiyar rayuka da dama tare da raba wasu da dama daga cikin mazauna yankin ciki har da ‘yan asalin Kano mazauna yankin.
A cewar sanarwar, kwamitin yana karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.
Karanta: A biya diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa, sannan a hukunta masu laifi – NBA ga gwamnan Edo
SolaceBase ta ruwaito cewa cikin tawagar akwai manyan mutane irin su Sarkin Rano, Ambasada Mohammad Isa Umar; Kwamishinonin Al’amuran Addini, Kananan Hukumomi da Masarautu, Ayyuka na Musamman da Harkokin Mata; Shugaban karamar hukumar Bunkure; da sauran manyan jami’ai.
Da yake jawabi a filin tashi da saukar jiragen sama na Mallam Aminu Kano kafin tashin jirginsu, mataimakin gwamna Gwarzo ya jaddada kudirin kwamitin na tabbatar da adalci, zaman lafiya da sulhu.
Ya kara da cewa, wannan mummunan lamari da ya faru a watan jiya, ya kara dagula al’amura a cikin al’ummar da abin ya shafa, don haka an tsara kwamitin zai tattauna da Gwamnan Jihar Edo, da shugabannin hukumomin tsaro, da sarakunan gargajiya, da kungiyoyin fararen hula a tsawon mako guda.