Hukumar kula da Wutar lantarki ta Najeriya (NERC) ta ci tarar Naira miliyan 628.03 kan wasu Kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) guda takwas saboda rashin bin ka’idojin tsarin farashin lantarki ga kwastomomin da ba su da mita a tsakanin watan Yuli zuwa Satumbar 2024.
Kamfanonin da abin ya shafa sun hada da Abuja, Eko, Enugu, Ikeja, Jos, Kaduna, Kano, da Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki na Yola.
Takunkumin ya biyo bayan Sashe na 34(1)(d) na Dokar Wutar Lantarki ta 2023 (EA 2023).
An ci kamfanonin tarar sama da naira miliyan 6287, sannan ana so su rage farashin lantarkin ga kwastomomin da abin ya shafa zuwa 15 ga watan Mayun 2025.
NERC ta ce wannan matakin da ta ɗauka yana cikin ƙudurinta ta tabbatar da ana bin doka da oda, tare da kare haƙƙin kwastomomi.